Tumfafiya wata bishiya ce mai matsakaicin tsayi da ke girma a Yammaci da Gabacin Afrika da kuma wasu sassa na Kudancin Asiya.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Haka kuma ana samun tumfafiya a kasar Indiya. Ta kuma kasance daya daga cikin bishiyoyin da cibiyar koyar da hada magani da ke a kasar ta India waton (All India Institute Of Medical Sciences) sun yi nazari na musamman ga wasu muhimman sinadiran da ke kumshe a cikin ganyen tumfafiya inda suka tabbatar da cewa wadannan sinadiran suna maganin gudawa.

Karanta>>> Yadda Zaki Haɗa Ingantaccen Maganin Ciwon Sanyi (Infection)

A dalilin haka ne masana maganin tsirran itatuwa na kasar Indiya waton ‘Ayurbedic pharmacopoeia’ suka yi umurni amfani da saiwar da kuma ganye ko kunnuwan tunfafiya a magance asma da daukewar sheda da kuma sauran cututtukan da ake dangantawa da cututtukan huhu.

A kasar Hausa, masu maganin gargajiya na amfani da ruwan tumfafiya don warkar da wasu cututtukan fata kamar makero. Inda ake aske gashin kai ko kuma duk inda makeron yake a jiki sai a karkare gurin da makeron yake har sai gurin ya yi jini, sai a tarfa wadannan ruwan na tumfafiya kan makeron, za a dunga wanke wajen a kullum ana sanya ruwan tumfafiya a sama har sanda ciwon ya warke.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Izinin Allah

Tumfafiya na maganin dafi kamar na maciji da cizon kunama. Ana amfani da saiwar tumfafiya bayan an konata, sai a gauraya garinta da na danyen mai a shafa kan inda cizon ko harbin yake.

A kasar India, suna amfani da furen tumfafiya ga masu farfadiya da kuma ciwon kurkunu. Ana amfani da kunnuwan tumfafiya a maida basir mai tsiro.

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

Za a nemi kunnuwan tumfafiya kamar kwara biyu ko uku haka, sai a dan kara su ga zafin wuta kadan sai a danne dubura da su in sha Allahu nan take duburar za ta koma.

Ana tarfa ruwan tumfafiya kamar digo biyu a cikin kunnen da ke ciwo za a yi haka sau daya zuwa biyu. Amma idan kunnen na ruwa to sai a tafasa itatuwan tumfafiyar misalin kofi daya sai a rinka wanke kunnen da ke ciwo da su.

Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

Tumfafiya na maganin dan kanoma wanda ya tsananta, shawara, ciwon ciki, yawan ciwon kai na ba gaira ba dalili, tarin nimoniya da kuma cutar kuturta.

Ana kona saiwar tumfafiya a maida su gari sai a hada da dan karamin cokali na garin lalle a daura a kan ciwon kafa ko hannu ko yatsan da ya kumbura ko ya ja ruwa kamar ciwon dan kankare ko wanda ake tunanin na kambun baka ne. Wannan kumshin zai zuke dafin ciwon a cikin karamin lokaci.

Karanta>>> Ga Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

Ana amfani da tumfafiya a kona jinnun da aka turo wa mutum ta hanyar sihiri. A nan za a nemi garin ganyen kaikayi koma kan mashekiya sai a nemi furen tumfafiya a shanya, idan ya bushe sai a dake a gauraya su waje daya a nemi allo babba a rubuta abun da ya sauwaka daga ayoyin Alkur’ani Maigirma sai a wanke a tafasa a sha tun da safe kamin a karya. Wallahi sihirin ko wane iri ne zai karye nan take.

Ana zubar da ciki nan take lokacin da aka yi amfani da tumfafiya. Amma ba za mu fadi yanda ake yin sa ba. Saboda lahaninsa da kuma damar da wasu za su samu ta aikata abin da bai dace ba.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Ana tafasa kunnuwan tumfafiya a tunga wanka da ruwan tun da safe dan maganin matsanancin ciwon gabobi da kuma jiyojin jiki.

Ana busar da furen tumfafiya sai a dake ya koma gari a rinka sha a cikin ruwan zafi duk lokacin da za a kwanta domin magance mutuwar zakari.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Ana amfani da kunnuwan tumfafiya dan dawo da jinin al’adan da ya dauke na tsawon lokaci. Ana turara kunnuwan tumfafiya dan warkar da asma da ciwon kai na gaban goshi.

A kan sanya ruwa a cikin kwallo bakwai na diyan tumfafiya, sai a bar ruwan sai sun kwana uku a ciki sai a juye ruwan a tarfa zuma cokali biyu a sha kamin a ci komai. Maganin sara na karfe kamar takobi ko wuka da rauni ko kariya mai tsanani ga jiki.

Ana amfani da ruwan tumfafiya wajen ciwon hakori. A nan ana diga ruwan tumfafiya a hakorin da ke ciwo.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Mata masu neman tagomashi ga mazajensu sai su nemi busasshen garin tumfafiya sai su hada da garin lalle da kuma garin ganyen bishiyar birana.

Sai dai kuma bishiyar tumfafiya tana da ban tsoro musamman da dare inda takan canza bishiya ce da iskoki ke fakewa a gunta. Dan haka sai a san yanda aka tinkaren ta. Amma tana da fa’idodi da dama. Duk da yake ba kowane irin ilmi ya dace mu fayyace ba. Saboda fadar wani ilmi zai zamo illa. Da fatar duk abin da muka fada a kan kuskure za a gafarce mu.

MAGANIN GYARAN NONO MAI SAUKIN HADAWA

Sharadin shine Ayi Sharing 🔔🔔

Wannan haɗine mai saukin gaske amma yana da matukar tasiri sosai yana ƙara girman nono sosai cikin ƙanƙanin Lokaci......

Sannan ga yan'mata waɗanda basuyi aure ba yana hana nono zubewa idan kina amfani dashi inshaAllah mamanki zasu kasance a tsaye ......

Ga waɗanda nononsu ya zaɓe ma'ana ya kwanta suyi amfani dashi na tsawon kwana uku zuwa bakwai zakusha mamakin yadda zasu ciko su tashi inshaAllah...

Sannan yana magance matsaloli irinsu : sanyin nono, ciwon nono da dai sauransu....

Sannan yana ƙara ruwan nono sosai gamai shayarwa....

YADDA ZAKU HAƊA MAGANIN

Kunemo wannan kwallon dake jikin iccen tumfafiya ga hotonshi nan kasan rubutun nan bayan kunnemoshi sai ku shanyashi a cikin rana , batare daya fashe ba . Idan ya bushe sai ku dakeshi ya koma gari .

Bayan kun dakeshi ya koma gari zakuga akwai wata kamar yana yana a cikin sa ita kaɗai zaku cire bayan kun dakeshi...... Sai kunemo ɗanyan mai (ma'ana ɗanyan man shanu) ku haɗasu waje guda a kwaɓasu sai Adunga shafawa a nonnon uwar gida zakisha mamakin yadda gabanki zai ciko tamkar na budurwa.....

wannan maganin cikin ƙan ƙanin lokaci yake kama jiki kuma baya da wata illa insha Allah

GARGADI

WANNAN MAGANIN BA'A SHANSA KAWAI SHAFAWA AKE YI

Rahotun Leadership a yau